Duk wasu masu rike da mukamin siyasa zasu sauka cikin kwanaki 30 kafin zabe, a cewar Kotu
Duk wasu masu rike da mukamin siyasa zasu sauka cikin kwanaki 30 kafin zabe, a cewar Kotu
Wata babbar kotun tarayya dake zama a Umuahia a jihar Abia ta umarci babban lauyan Gwamnatin tarayya Kuma ministan Shari’a da ya gaggauta soke sashe na tamanin da hudu 84 (12), na sabuwar dokar zabe kamar yadda gidan
talabijin na Channels ta ruwaito.
Mai shari’a Evelyn Anyadike, a yau Juma’a tace, sashin ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar ba ya kan ka’ida, sannan kuma yaci karo da tanadin kundin tsarin mulkin kasar.
Sashen yana cewa, babu wani nadadde da zai zaba ko a zabe shi a wani mukami a cikin jam’iyyar ba tare da ya ajiye mukamin sa ba
kwanaki talatin 30 kafin zabe.
A cikin karar mai lamba FHC/UM/CS/26/2022 mai Shari’a Anyadike ya kara bayyana cewa, sashe na 66 (1) (f),107(1)(f),137(1)(f)da182(1)(f) ) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya rigaya ya
bayyana cewa.
Masu Nadaddu a mukaman Gwamnati da suke son tsayawa takara zasu sauka daga kan mukaminsu akalla kwanaki talatin 30 kafin ranar zabe, kuma duk wata doka da ta tilasta wa wadanda aka nada suyi murabus ko barin ofis a kowane lokaci kafin hakan ta saba wa kundin tsarin mulki.
Yayin da yake rattaba hannu kan kudurin dokar zabe a watan da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar kasar nan data soke sashe na tamanin 84 (12) bisa dalilan rashin baiwa masu rike da mukamai hakkinsu.
Sai dai majalisar dattawan taki yin la’akari da bukatar shugaban kasar kuma tayi watsi da kudirin na neman ayi wa sashen kwaskwarima.
Daga Daily Nigerian Hausa.