Labarai

Kungiyar Izala ta jihar Neja ta tallafawa ‘yan gudun hijira da kayan abinci da suturu domin rage radadi

Kungiyar Izala ta jihar Neja ta tallafawa 'yan gudun hijira da kayan abinci da suturu domin rage radadi

Kungiyar Izala dake jihar Neja ta tallafawa ‘yan gudun shijira da kayayyakin abinci kala-kala kungiyar ta bada wannan tallafi ne ga ‘yan gudun hijira dan rage masu radadin da suke fama dashi na rayuwa, sakamakon iftila’in da ‘yan ta’adda suka jefa su a ciki har ma suka raba su da garuruwan su.

shugaban kungiyar Izala ta jihar Neja Alhaji Abdullahi Musa Mai Radiyo Shi ya jagoranci kaddamar da wannan tallafin da aka yiwa ‘yan gudun shijirar, na kayayyakin abinci da kuma kayan sawa da suka hada da irin su.

Shinkafa buhu 113
Semovita 100
Wake buhu 10
Masara buhu 5
Dawa buhu 1
Taliya Caton 105
Madara Caton 100
Sugar buhu 20
Indomi 210
Manja Jarka 20
Mangyada 50
Tabarma 250
Atamfa turmi 203
Sai kayan sawa na maza da mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button