Labaran Kannywood

Turkashi: Wani faifan Bidiyon daya daga cikin iyaye a kannywood na rawa da mata ya dau hankula.

Wani faifan bidiyon daya daga cikin jarumai iyaye a masana’antar Kannywood Tahir Fagge kenan suna rausayawa acikin wata wakar hausa mai taken (Munafiki baiyi ba) shida wasu yan matan masana’antar Kannywood.

Saidai tun bayan bayyanar wannan bidiyon dai aketa cece kuce akan rashin kyawun wannan bidiyon, ganin yadda Tahir Fagge a matsayinsa na uba baikamata yafito yana rawa da yan matan da yama haifesu ba acewar mutane.

Yanayin bidiyon ya bayyana cewar an daukesa sane awani wajen da ake kan daukar wani sabon shirin hausa, saidai har izuwa yanzu jarumin baifito yayi magana ba akan korafin da mutane sukeyi.

https://youtu.be/psf3MzLTydE

Ku cigaba da bibiyar mu dan samun zafafan labarai da wakokin Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button