Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wasu ‘yan ta’adda suka kone matar aure mai juna biyu tare da dan ta bayan sunje neman kudi basu samu ba

Yadda wasu 'yan ta'adda suka kone matar aure mai juna biyu tare da dan ta bayan sunje neman kudi basu samu ba

A jiya Alhamis ne wasu ‘yan ta’adda suka kai hari wani gari mai suna “Maikujera” dake karamar hukumar Mulkin Rabah a jihar Sokoto.

Advertising

Majiyar Hausaloaded ta sami damar zantawa da wani mutumi mazaunin garin inda yake bayyana abin da ya faru, inda aka kashe wani mutumi tare da matar sa wanda take dauke da juna biyu da kuma dan karamin yaran su.

Magajinsa mutum ne da yake namomi a ciki garin maikujera wanda yake noma albasa cikin ikon Allah tayi kyau sosai, to shine ya aika a saya kuma an sayar to shine jiya Alhamis wanda yake baiwa albasar ya kawo masa kudi.

Bayan dare ya yi barayi suka shiga cikin gidansu inda sunka tarar da gidan babu kudi babu mai kudin, inda ya gudu daga gidan duba da yasan tabbas tunda suka san an kawo masa kudi za’a zo nemansa sabida akwai barazanar rashin tsaro.

Advertising

To shine sunka bincike sunka tabbatar da cewa tabbas wanda suka zo nema baya gidan shine kanen sa da matar sa mai juna biyu da kuma dansa, suna kwance cikin daki suka bude suka dauko harawa sunka kunna mata wuta sannan suka jefa a cikin dakin.

Wanda shine sanadiyar mutuwar matar mai juna biyu da kuma karamin dan ta, bayan da ‘yan ta’addan suka kunna musu wuta suka cikin daki.

Allah ya jikansu yayi musu rahama Amen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button