Advertising
Advertising
Labarai

Zamu fice daga jam’iyyar APC matukar Buhari bai janye goyon bayan sa ga Mai Mala Buni ba, cewar Nasiru El-Rufa’i

A wani labari da muka samu daga shafin Daily News Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facebook Gwamna Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa.

Advertising

Zasu fice daga jam’iyyar APC matukar shugaba Muhammad Buhari bai janye kalaman sa na nuna goyon baya a bangaren Gwamna Mai Mala Buni kan shugabancin jam’iyyar APC ba.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i ya bayyana cewa, baza su taba yarda da matakin da Buhari yake shirin dauka na dawo da Mai Mala Buni kan kujerar shugabancin jam’iyyar APC ba.

Nasiru El-Rufa’i yace, lallai dole ne Gwamna Mai Mala Buni ya sauka daga wannan matsayi tare da barma Gwamnan Neja Sani Bello, Gwamnan ya yi barazanar barin jam’iyyar matukar aka ce za’a cigaba da yin wannan rashin adalci.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button