Advertising
Advertising
Labarai

Sau 15 a jere ina yin gobara kuma duk ta cinye min kaya na dana marayun da suke waje na, cewar Hauwa uwar marayu

Wata mata mai suna Hajiya Hauwa Mai kitso dake zaune a unguwar Kadawa dake Karamar Hukumar Gwale ta jihar Kano ta koka kan cewa gobara ta addabe ta.

Advertising

Duk da har yanzu ba’a san daga ina matsalar
take ba amma al’umma sun fara hasashen cewa, ko aljanin nan mai suna Batoyi ne ke hada mata gobarar, duba da cewa wutar ce ke tashi ba tare da wani musabbabi ba.

A lokacin da take zanta wa da tashar Rahma Radio a Kano Hajiya Hauwa tace, sau goma sha biyar kenan wutar tana tashi, inda tace ko ta kai
kayan nata wani gida sai wutar ta bisu can ta kone su.

A cewar Hajiya Hauwa, tayi iya bakin kokarin ta kuma gashi duk kudaden ta da kayan ta sun kare, cikin alhini da damuwa Hajiya Hauwa take cewa ga marayu ina tare da su nice cin su nice
shan su suma kayan su duk sun kone.

Advertising

Kuma irin kwancen kayan nan da al’ummar Annabi suke taimaka mana da su suma sai kone
wa suke yi, Na rasa inda zan saka kai na ina dai ta addu’a wasu sun ce ko aljanin Batoyi ne to ni dai Allah ne masani.

Hajiya Hauwa tace, Ina dai rokon taimakon al’umma da’a kawo min dauki dan Allah dan Annabi.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button