Saudiya ta kaddamar da manhajar neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula Birtaniya
Saudiya ta kaddamar da manhajar neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula Birtaniya
Kasar Saudi Arebiya ta kaddamar da wata manhaja ta neman bizar Hajji da Ummara ta wayar salula a Birtaniya.
Saudiya ce kasa ta farko a duniya data kirkiro da hanyar yin rijistar biza ta wayar salula Daily Nigerian Hausa ta gano cewa, sabuwar manhajar zata baiwa maniyyaci dama ya shigar da duk bayanan sa da hotuna, ya kuma ajiye su kafin ya je ofishin buga bizar domin karbo wa.
Sai dai kuma dole ne bayanan da maniyyaci ya bayar a manhajar ya kasance ya yi daidai da wanda zai kai ofishin buga bizar.
An kirkiro da wannan sabuwar hanyar domin
saukaka hanyoyin kula da boda a Birtaniya tun a bara ne dai Ministan Harkokin Waje na Saudiya, Faisal bin Farhan ya kaddamar da manhajar bisa umarnin Yarima Muhammad Bin Salman.
Manhajar kuma ta samu ne da hadin gwiwar
hukumomi da dama na harkokin Hajji da Umara a Saudiya.