Sojoji sun budewa matata wuta bayan sun bukaci ta cire kayan jikin ta tsirara taki, cewar Sheikh Ibrahim Zakzaky
Sojoji sun budewa matata wuta bayan sun bukaci ta cire kayan jikin ta tsirara taki, cewar Sheikh Ibrahim Zakzaky
Shugaban kungiyar Mazahabar Shi’a Sheikh Ibrahim Zakzaky ya yi zargin cewa, jami’an tsaron da suka bude wuta a kansa da mabiyansa sun nemi matarsa tayi tsirara.
Ibrahim Zakzaky ya cigaba da cewa, wasu jami’an tsaro ne guda hudu 4 dauke da makamai suka shiga karamin dakin da yake shi da iyalan sa suka yi ta luguden wuta a shekarar 2015.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da yayi da BBC Hausa, Fiye da shekara shida ke nan tun bayan rikici tsakanin mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiyansa sun tare musu hanya a garin Zaria.
Inda ya kara da cewa, jami’an tsaron sun kashe daruruwan mutane kafin su kai kansu suna budewa daki suka ganmu suka ce, ga wasu nan ita matata suka ce mata ta cire kayanta da tace ba zata cire ba suka ce a bude wuta.
Ga cikekkiyar bidiyon nan a kasa domin ku kalla.