Labarai

Wani Mutumi ya mutu nan take a ya yin da ake shari’a a Kotu zai bada shaida kan wani Fili

A makon da ya gabata ne wani abin al’ajabi ya faru a wata kotun shari’a a garin mararranba Nyaya dake kan iyakar Abuja da Jihar Nasarawa, inda wani mutumi ya yanke jiki a kotun ya fadi nan take ya mutu a lokacin da Alkalin kotun ya kira shi da yazo ya bada shaida.

Mutumin da ya fadi ya mutu a kotun yaje bada shidar wani abokin sa ne da wata mata take zargin ya cinye mata filin ta a garin mararraba Nyaya, inda har lamarin ya kai su ga kotu domin gano gaskiyar al’amari.

A nan ne Alkalin Kotun ya kira mutumin domin yazo ya fadi abin da ya sani game da filin matar zuwan kenan bayan da Alkalin ya tambaye shi ko mai ya sani game da filin matar da take zargin an cinye mata, ya bude baki kenan zai yi magana sai kawai ya yanke jiki ya fadi inda yace ga garin ku nan ya mutu a cikin kotun.

Bayan faduwar tasa ne sai aka yi kiran gaggawa ga likitoci domin su duba halin da yake ciki nan take suka tabbatar da cewa ya mutu, inda Alkalin ya tashi daga zaman shari’ar da ake a ranar sabida ganin abin al’ajabin da ya faru.

Mutanen da suka halarci Kotun a yayin zaman shari’ar sun yi matukar mamakin abin da ya faru inda kowa yake tunanin wata ayace Allah ya nuna akan lamarin, wanda hakan ya kamata ya zama darasi ga mutanen da suke shaida zur akan abin da basu da masaniya a kai amma sabida rashin tsoron Allah da son abin duniya su fadi abin da basu sani ba.

Muna rokon Allah ya kare mu daga yin shaida zur kan fadin abin da bamu da masaniya a kai.

Rahoton Hausablog.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button