Wasu ‘yam mata guda 2 sun kubuta daga hannun ‘yan bindiga bayan sun sace su sun kaisu cikin daji
A ranar laraba 15/3/2022 da misalin 12:00 na dare wasu ‘yan bindiga suka kai hari Yasu-Yasu wani kauye mai nisan 2km daga garin Batsari a jihar Katsina.
‘Yan bindigar sunbi bi gida gida sun kwace wayoyin hannu kudi sutura da wani dan akuya da suka samu a wani gida, sunyi ma mutane da dama dukan tsiya sannan kuma sun tafi da wasu ‘yam mata guda biyu 2 Mubaraka Naziru da Amina Rabiu.
A hirar da aka yi da ‘yam matan bayan sun kubuta daga hannun ‘yan bindigar sun bayyana cewa, a lokacin da suka tafi dasu sun shaida masu cewa su kwantar da hankalin su da sunje wurin oga za’a aurar da su.
Sai dai cikin taimakon Allah suna isa da ‘yam matan maboyar tasu sai suka kawo masu lemun roba da burodi suma kuma suka sha wasu kwayoyi da lemun daga nan barci ya kwashe su.
Majiyar tace, ‘yam matan sun tashi suka kama hanya cikin matsanancin dare suna gudu basu san inda zasu baga kayar sarkakiya da sauran su, inda suka doshi wani tsauni suna tsammanin gari ne amma da isar su suka ga ba haka ba.
Daga nan suka sake bin hanyar har suka isa rugar wani bafullatani cikin tsoro suka isa gidan suna neman taimako sai yace suyi hakuri domin sun taba taimaka ma wasu, amma sai aka wulakanta su sai suka nuna masu hanyar Muniya ta karamar hukumar Safana.
Suka kama hanya da suka isa Muniya suka bayyana halin da suke ciki sai mutanen gari suka taimaka masu inda har wani ya basu tufafi, sannan suka kawo su gida cikin aminci.