Labarai
An daura auren Muhammad Ahmad Salihu mai shekaru 18 tare da Amaryar sa Sumayya Adam Ibrahim mai shekaru 16
A ranar juma’a ne a garin Tulden Fulani dake karamar hukumar Toro a jihqr Bauchi aka daura auren wani matashin saurayi mai shekaru 18 mai suna Muhammad Ahmad Salihu da Amaryar sa Sumayya Adam Ibrahim mai shekaru sha shida 16.
Kamar yadda muka sami rahoton daga shafin Hausaloaded bayan shafin Facebook mai suna Daily News Hausa sun ruwaito.
An daura auren Muhammad Ahmad Salihu da Amaryar sa Sumayya Adam Ibrahim a babban Masallacin Izala a garin Tulden Fulani, inda aka gudanar da shagulgulan bikin su cikin annushuwa da farin ciki.
Muna rokon Allah ya basu zaman lafiya mai dorewa tare da zuri’a ta gari.
Ga hotunan Angwan nan a kasa domin ku kalla.