Advertising
Advertising
Labarai

Baza mu hana Kwankwaso, Atiku da sauran masu bukata sayan fom din takara ba a shekarar 2023, uwar jam’iyar PDP

Baza mu hana Kwankwaso, Atiku da sauran masu bukata sayan fom din takara ba a shekarar 2023, uwar jam'iyar PDP

Uwar Jam’iyar PDP ta kasa tace har yanzu bata tsaida matsaya a kan ko wanne bangare ne na kasar nan zai fitar da dan takarar shugaban kasa ba.

Advertising

Inda take cewa, ta yanke shawar fara sayar da fom din takara ne domin kada ta sabawa wa’adin da hukumar zabe ta Kasa mai zaman Kanta “INEC” ta sanya.

Shugabancin jam’iyar ya bayyana cewa, sabida
jadawalin da “INEC” ta fitar shi ya sanya ba’a hana kowa ya sayi fom ba, musamman ma
Abubakar Atiku da Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Tuni Atiku ya sayi fom din takara wanda kudinsa ya kai Naira Miliyan dari hudu 400, inda yace wata kungiyar yan kasuwa a Arewa ce ta sayar masa.

Advertising

Bayan Atiku da Kwankwaso, Gwamna Aminu
Waziri Tambuwal na Sokoto da Gwamna Bala
Mohammed na Bauchi, suna neman takarar
Shugabancin kasar a jam’iyar ta adawa ta
PDP.

Haka zalika gwamnonin “PDP” na shiyyar kudu
sun bi sahun ‘yan uwan su na APC wajen tsaya wa akan cewa, dole dan takarar shugabancin kasa daga bangaren su zai fito.

Kamar yadda Daily Nigerian Hausa suka wallafa rahoton.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button