Advertising
Advertising
Labarai

Kamata yayi kasashen Afrika su fito a gwabza yakin Ukraine dasu kada su zama ‘yan babu ruwan mu

Kamata yayi kasashen Afrika su fito a gwabza yakin Ukraine dasu kada su zama 'yan babu ruwan mu

Jakadiyar Amurka ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, bai kamata kasashen Afrika su zama ‘yan ba ruwansu a yakin Ukraine ba.

Advertising

A yayin wata hira da BBC Linda Thoma Greenfield ta bayyana cewa, a kuri’ar da aka yi a babban zauren majalisar makonni biyu da suka gabata kan kin amincewa da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.

Inda tace, kasashe 17 sun ki daukar bangaren sai kuma kasashe takwas sun kaurace wa jefa kuri’ar baki daya.

Jakadiyar ta kara da cewa babu batun zama ‘yan ba ruwansu a wannan lamari kuma wannan yakin ba yakin caccar baka bane tsakanin kasashen Yamma da Rasha.

Advertising

Ms Greenfield ta kuma ce kasarta zata mara baya ga kudurin Afirka ta Kudu na shiga tsakani a yakin na Ukraine.

A cewar wani babban jami’in Sojan Amurka, dakarun Kasae Rasha sun kasa yin gaba a Ukraine amma har yanzu suna da karfin dakarun kusan casa’in 90 cikin dari 100.

A cikin wata sanarwa jami’in ya bayyana cewa, dakarun Kasar Rasha sam basu sami wani cigaba ba zuwa birni Kyiv, sannan kuma babu wani motsi da suka yi zuwa gabashin birnin.

Sun ce jajircewar dakarun Kasar Ukraine ne dalili amma har yanzu birnin Mariupol da aka yi wa zobe yana nan yadda yake, muna cigaba da ganin luguden wuta a can tun bayan fara yakin, a cewar jami’in.

A cewar sa, Kasar Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da dubu daya da tamanin 1,080 tun daga farkon yakin, inda sanarwar tace rahoton harin da aka ce an kai kusa da filin jirgin sama na birnin Lyviv da kanshin gaskiya a cikin sa, amma babu tabbas kan irin barnar da ya yi zuwa yanzu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button