Advertising
Advertising
Labarai

Matata ta hana ni yin jima’i da ita kuma na sha kamata tana kallon bidiyon batsa da hotuna, cewar wani magidanci

Matata ta hana ni yin jima'i da ita kuma na sha kamata tana kallon bidiyon batsa da hotuna, cewar wani magidanci

Wani injiniya mai suna Godwin Nwali ya garzaya wata kotun gargajiya ta Igando dake jihar Legas inda yake bukatar Kotun ta raba aurensa da matarsa mai suna ​​Nsika.

Advertising

Godwin Nwali ya yi zargin matar tasa ba ta da hankali kuma idan ya nemi ya yi jima’i da ita sai ta hana shi lamarin da yake faba masa rai ke nan.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya “NAN” ya ruwaito cewa, Godwin Nwali ya kara da cewa matar tasa tana kallon hotunan batsa kuma tana yin wasu sha’anin aure.

Ya cigaba da cewa, matata ba ta damu da ni ba ba ta da alhaki kuma tana tattaunawa da maza daban-daban a Facebook, na kama ta tana kallon batsa a wayarta.

Advertising

Amma matar tasa mai suba Nsika ta musanta duk wani zarge-zarge da mijin nata yake mata, inda take cewa.

Ni mace ce mai hakki kuma mata ina kula da gidana, ni bani da matsala kamar yadda yake zargi bana shiga cikin al’amuran da suka wuce aure sabida ya sabawa al’adarmu a Akwa Ibom.

Ta kara da cewa, bani da fushi mijina ne mai tashin hankali nice nake da alhakin ciyar da gida da biyan kudin makarantar yaran mu.

Sannan ta bayyana cewa, mijinta ya yi karyar cewa tana hana shi yin jima’i da ita, lokacin da na haifi yaronmu na sami matsala a cikin farji na kuma an shawarce ni da in daina jima’i na wani lokaci.

An gayyace mu kauye don sasanta rikicinmu amma mijina ya ki zuwa bana adawa da a raba aurenmu, bani da sha’awar auren.

Alkalin kotun “Mista Adeniyi Koledoye” ya dage sauraron karar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button