Advertising
Advertising
Labarai

Diyar Shugaban Kasa Hanan Buhari tare da Mijinta Muhammad Turad sun sami karuwar da Namiji

Diyar Shugaban Kasa Hanan Buhari tare da Mijinta Muhammad Turad sun sami karuwar da Namiji

Diyar shugaban Kasa Muhammad Buhari Hanan ta haifi danta namiji inda kuma muka sami labarin cewa, daga uwar har dan nata suna cikin koshin lafiya.

Advertising

Shafin insragram mai suna mr_mrs_arewa ya tattaro cewa, Muhammad Turad mijin Hanan Buhari ya sanar da labarin karuwar da suka samu shi da matar sa Hanan a shafin sa.

Inda ma ya bayyana cewa, sun sanyawa dan nasu suna Zayd kamar yadda Legit ta ruwaito.

Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari Hanan tare da mijinta Muhammad Turad Sha’aban, Allah ya albarkacesu da haohuwar da namiji a kasar Turkiyya.

Advertising

Wata majiya ta kusa da iyalan ta sanar da cewa, an haifin dan ne a ranar Lahadi 20 ga wannan watan da muke ciki na Maris.

Muhammad Turad mijin Hanan Buhari ya bayyana sanarwar karuwar da suka samu a shafin sa kamar haka.

Allah ya azurta ni da matata da haihuwar da namiji! Alhamdulillah. “Mun saka masa suna Muhammad Zayd (Hibbu Rasulallah).

Idan zaku iya tunawa Hanan Buhari ta auri Muhammad Turad ne a watan Satumban 2020, a wani gagarumin shagali da aka yi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button