Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a wasu kananan Hukumomi 2 Jema’a da Kaura

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci a wasu kananan Hukumomi 2 Jema'a da Kaura

A wani labarin da muka samu a yanzu munji cewa, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar ta baci ta tsawon sa’o’i 24 a kananan Hukumomin Jema’a da Kaura, inda ta ce tuni dokar ta fara aiki.

Advertising

Sanarwar na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke dasa hannun Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan.

Sanarwar ta bayyana cewa, an dauki wannan mataki ne biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar da kuma taimakawa jami’an tsaro don daidaita al’amura da kuma dawo da doka da oda a yankunan.

Ta kuma kara da cewa, hukumomin tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar ta bacin inda gwamnati tayi kira ga daukacin mazauna kananan Hukumomin Jema’a da Kaura, dasu baiwa jami’an tsaro hadin kai domin dawo da zaman lafiya da bin doka da oda cikin gaggawa.

Advertising

Haka zalika sanarwar tace, gwamnati tayi Allah wadai da tashe-tashen hankula da kuma duk wasu ayyukan ta’addanci da suka afku a yankin, domin za’a fitar da karin bayani nan gaba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button