Advertising
Advertising
Labarai

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nuna damuwar sa kan hare-haren ‘yan kungiyar IPOB a Imo

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya nuna damuwar sa kan hare-haren 'yan kungiyar IPOB a Imo

A wani labari da shafin Daily Nigerian Hausa suka ruwaito Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya nuna damuwa a bisa hare-haren ‘yan
haramtacciyar kungiyar masu rajin samar da
yankin Biafra “IPOB”.

Advertising

Idan zaku iya tuna cewa, a ranar Asabar ne ‘yan kungiyar IPOB suka kai hari gidan Shugaban Ohaneze Ndigbo, Ohanaeze Ndigbo, Farfesa George Obiozor, a Awo-Omanma, Karamar Hukumar Oru ta kudu.

A wata sanarwar da kakakinsa Garba Shehu
ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, Buhari ya yi Allah wadai da harin, inda ya yi kira kan cewa a zauna lafiya.

A cewar sa, ana nan ana duba da gyara yanayin doka da oda a shiyyar Kudu maso Gabas, shi yasa Shugaba Muhammad Buhari ya yi kira ga al’ummar Jihar Imo, musamman da kuma na shiyyar gaba daya dasu zauna lafiya domin ‘yan sanda na kai komo don samar da zaman lafiya.

Advertising

Sannan kuma Shugaba Buhari ya jajanta wa ‘yan sanda bisa rashin jami’ai da kayan aiki dasu ka yi, inda ya kuma jajanta wa Obiozor wanda ya yi kira gare shi da ya cigaba da aikin sa na samar da zaman lafiya da hadin kai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button