Labarai

Turkashi: Dalibin Nijeriya da ya guje wa yaƙi a Ukraine ya rasu a Sokoto

Wani Dalibi da ke karatu a Ukraine mai suna Uzaifa Halilu ya rasu bayan kakanni biyu da dawo wa gida Sokoto bayan ya guje wa yakin da Ukraine ɗin ke yi da Russia.

Rahotanni sun baiyana cewa, kafin dawowarsa gida Jihar Sokoto, Modachi ya kai shekaru uku bai zo hutu ba da ga Ukraine, inda ya ke karatu aJami’ar Ilimin Lafiya ta Zaporozhye a ƙasar.

Mahaifin dalibin, Habibu Halliru Modachi, ya ce ɗan nasa, wanda ya ke a shekarar ƙarshe a jami’ar, ya rasu, kuma Allah ne Ya ga dama ya dauke shi.

A cewar mahaifin, wanda dan majalisar jiha ne, ya ce Allah ne Ya bashi ɗan kuma Ya karɓe abinsa.

Ya kara da cewa da Ukraine din dan nasa ya rasu, da an fadi maganganu da dama cewa sojojin Russia sun kashe shi ko ma sojojin Ukraine sun kashe shi bisa rashin sani.

Bayan ya masa addu’a a kan Allah Hai masa Rahma, mahaifin ya kuma gode wa Allah da Ya sanya ya rasu a gaban iyayensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button