Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Kafin a saka ni a fim har wankin wandon mata nayi da rikon jaka cewar Naburaska

Fitaccen jarumin Borkwanci a Masana antar shirya Finafinan Hausa Mustapha Naburaska wanda yayi kaurin suna wajen nishadantar da masu bibiyar finalinan hausa.

Advertising

A wata tattaunawa da akayi da jarumin acikin shirin dandalin taurarayi na tashar Arewa24 ya bayyana cewa Daya shigo cikin Masana’antar to Kannywood aiken farko da aka sakashi yayi shine siyo sigari.. Sannan a cikin Jaruman Kannywood mata akwai wanda har wanki da guga yayi masu.

Wanda acikin kayan da yake wankewa harda pant da bireziya sannan ya zama dan rikon jakar hannu na wata fitacciyar Jaruma a Masana’antar wacce be bayyana Sunan taba. Baya ga haka kuma yaje wajen daukar wata waka ta wani babban darakta me suna Rabiu Ibrahim HRB wanda wannan jaruma da yake rikema jaka ta nema masa alfarma abashi dama shima ya gwada tasa basirar.

Sai dai hakan bata samu inda daraktan ya bayyana cewa Allah shi kiyaye domin bashi da wajen da zai sashi ya gwada basirar sa.

Advertising

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button