Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan Kwankwasiyya sun yi gangami a wajan zaben shugabannin Jam’iyyar NNPP a jihar Kano

'Yan Kwankwasiyya sun yi gangami a wajan zaben shugabannin Jam'iyyar NNPP a jihar Kano

Dubban yan Kwankwasiyya ne suka mamaye
harabar wurin da Jam’iyyar “NNPP” Mai kayan
marmari zata gudanar da babban zabenta.

Advertising

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa, an tsara
gudanar da zaben ne a cibiyar koyar da sana’o’i ta sani Abacha wato Abacha Youth Center dake kan hayar Madobi.

Ana sa ran Jam’iyyar zata zabi shugabaninta
a mataki daban daban, sai dai abinda ke jan hankali a wurin taron shi ne yadda magoya bayan Kwankwasiyya suka mamaye wurin.

Wannan dai baya rasa nasaba da yadda ake ta rade-radin jagoran Kwankwasiyya “Rabiu Musa Kwankwaso” zai koma cikin Jam’iyyar zuwa nan da karshen watan Maris.

Advertising

Idan za’a iya tunawa dai tun a watan da ya gabata ne Jam’iyyar ta rushe shugabancinta, tare da kafa kwamitin riko.

A jiya Litinin ne dai a ke gudanar da zaben
shugabannin Jam’iyyar da kuma ake ganin ‘yan kwankwasiyya ne suka mamaye dukkannin mukaman da za’a raba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button