Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ko kunsan cewa wannan shine dalilin da yasa aka daina ganin Wadannan Jaruman acikin Fim kuma suka hakuri da harkar

Wasu dalilai da yasa aka dena ganin wasu jaruman kannywood guda biyu a cikin fina finan Hausa.

Advertising

Tashar arewapakage Tv ta hada mana cikaken Rahoto kan wannan al’amari kasancewar ana dena ganin wasu jaruman a cikin fina finai ba tareda sanin dalili ba hakan yasa tashar ta fitar da dalilin dayasa aka dena ganin su a cikin fina finan.

Bilkisu Abdullahi Shema fitacciyar Jaruma wacce yar garin karamar hukumar dutsen mace ta jahar katsina, bilkisu shema na cikin jerin Fitattun mata da sunan su ya shahara a Masana’antar Kannywood.

Duk da Kasancewar bata fito a Finafinai masu yawa ba anfi saninta acikin vedion wakoki, sai dai yawancin finafinan data fito sun shahara matuka hakan yasa tadaukaka..

Advertising

To sai dai an shafe wasu shekaru rabonda aji duriyar jarumar a Masana’antar domin abubuwa da dama sun faru wanda suka hada da bukukuwa da akayi da wasu shagulgulan amma duk da hakan ba aga fuskar jarumar ba a wannan wurare.

Masoyan ta da dama harma sun gaji da tambaya kasancewar basa samun amsar data dace da tambayar su, to sai dai a wata hira da akayi da jarumar ta bayyana cewa tun bayan fim dinta na farko taso tayi aure to sai dai Allah bai nufa hakan ba.

Bayan faruwar hakan ne sai kuma aka daina ganin fuskar jarumar kwata kwata a Masana’antar wanda muna tunanin hakan na nuna cewa akwai wasu ayyuka dake hanata Harkar ta fim da kuma wani shiri dake yiwa rayuwar ta kasan cewar dama tin farko taso tayi aure sai dai Allah bai nufa hakan ba.

Jaruma ta biyu.

Yawancin finafinanta tana fitowa ne a kampanin 2effects empire wanda wannan kampani mallakin jarumi sani danja ne da yakubu Muhamma.

Amma yawancin mutane sun santa ne acikin shiri me dogon zango Yan zamani wanda suka fito tare da wasu. manyan jarumai, An shafe kusan shekaru uku kenan rabonda aga fuskar jarumar acikin finafinai, harma abokan Sana’ar nata ba kowa yasan dalili ba..

Sai dai kuma ana yawan ganin jarumar tana wallafa Hotunan ta a shafinta na Instagram daga bangkok babban birnin kasar Thailand, Hakan yasa akaita tamabayar jarumar dalilin da yakaita kasar amma bata bada amsar hakan ba.

Sai dai a shekarar 2019 Mujallar Fim tayi hira da jarumar inda ta bayyana masu dalilin daya sa aka aka daina jin duriyar ta a Masana’antar, ta kuma wata mujjalar tace tayi aure ne tun a shekarar 2018 kuma anyi auren ne a asirce hakan yasa ba kowa ya sani ba.

Sannan bayan daura aure rashida ta koma kasar Thailand inda acan ne mijin nata yake da zama, wannan dai shine dalikin da yasa aka daina ganin jarumar a Masana’antar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button