Kotu ta garkame wani matashi mai suna Gharzali a gidan yari bisa zargin dukan wata Mata mai shekaru 55
A wani labari da muka samu a yanzu daga shafin Daily Nigerian Hausa dake kan kafar sada zumun ta ta Facebook, sun ruwaito wani labari kan cewa.
Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba
1 da ke 2amanta a kofar kudu, karkashin
jagorancin Malam Ibrahim Sarki Yola, ta aike
da wani matashi gidan yari mai suna Ghazali Abdullahi Goron Dutse, bisa zargin sa da dukan wata matar aure mai suna Halima Abdulhamid
mai kimanin shekaru 55 a duniya.
Lamarin ya faru ne bayan wata hatsaniya data shiga tsakanin su a unguwar Kuntau dake yankin Karamar Hukumar Gwale ta jihar Kano, lokacin da Ghazali wanda ake wa lakabi da Ghaza ya sayi sabuwar mota.
Gharzali yana cikin nuna wa yan uwa da abokan arziki motar ne kuma yana ta danna kararrawar
motar har ya damu Halima, har ta yi masa
magana sai kuma rikici ya shiga tsakani har ya kai ga ya mata duka nan take.
Daga bisani sai ta kai kara caji ofis domin abi mata hakkinta, Sai Kuma bayan dan sanda mai gabatar da kara “Sifeto Suleman” ya gama karanta wa wanda ake kara kunshin tuhume tuhuman da ake yi masa, sai ya musanta wasu daga ciki amma kuma ya amsa cewa yace mata
mutuniyar banza da kuma dukan ta.
Bayan jin ko wane bangare Alkali Sarki Yola
ya yi umarni ga jami’an gidan yari dasu tafi da Gharzali gidan yari su ajiye shi har zuwa ranar 16 ga watan Mayu domin cigaba da sauraron
karar.
Cikin kwalla Hajiya Halima ta bayyana wa manema labarai cewar, ko shakka babu Ghazali yaci zarafin ta a bainar jama’a, inda ta kuma
nuna farin cikin yadda kotun ta fara nema mata hakkin ta.
Sannan Hajiya Halima tayi kira ga mahukuntan dasu shigo cikin wannan alamarin domin ganin an kwatar mata hakkin nata na cin zarafin da Gharzali ya yi mata ta hanyar duka da ake zargin ya yi mata.