Advertising
Advertising
Labarai

Wata Mata ta kashe ‘yar cikinta mai shekaru 10 ta hanyar cinna mata wuta

Wata Mata ta kashe 'yar cikinta mai shekaru 10 ta hanyar cinna mata wuta

Wata mata mai ‘yaya biyar 5 ta watsa wa ’yar cikinta man fetur sannan ta sa mata mata wuta sabida ’yar ta dauki wayar da mahafiyar ta boye, lamarin ya faru ne a Jihar Ogun.

Advertising

‘Yan sanda daga Babban Ofishin ’Yan Sanda na Mowe a Jihar Ogun sun tsare matar ne bayan wani makwacinta ya kai musu kara kan cewa, matar ta banka wa ’yar cikinta mai shekara 10 wuta da gangan.

Makwabcin da suke zaune a gida daya ya shaida wa ’yan sanda cewa, matar ta yi wa ’yarta danyen aikin ne sabida wayar dan uwan yarinyar da ta dauko ta ba shi bayan mahaifiyar ta kwace wayar daga hannunsa ta boye.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya bayyana cewa, bayan samun labarin ne DPO na Babban Ofishin ’Yan Sanda dake Mowe, CSP Folashade Tanaruno, tare da jami’an binciken kwakwaf daga ofishin suka je suka cafke matar.

Advertising

Sannan yace, da aka titsiye matar wadda tace sun rabu da mahaifin yaran ta bayyana wa ’yan sanda cewa, bata san abin da ya hau kanta ba a lokacin da ta yiwa ’yarta hakan.

Oyeyemi ya bayyana cewa, an garzaya da yarinyar zuwa asibiti mafi kusa inda daga nan aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo domin samun kulawar da ta dace.

Ya kara da cewa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun Lanre Bankole ya sa a tsare matar a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button