‘Yan sanda a jihar Kano na shirin kama wani shahararran mai sharhi akan siyasa Bashir Jentile akan zargin sukar Gwamnan jihar
'Yan sanda a jihar Kano na shirin kama wani shahararran mai sharhi akan siyasa Bashir Jentile akan zargin sukar Gwamnan jihar
A yanzu muka sami labarin cewa, Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano na shirin cafke wani shahararren mai sharhi kan al’amuran siyasa “Bashir Gentile” akan zargin sukar gwamnan jihar “Abdullahi Ganduje” a wasu shirye-shiryen rediyo, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito.
Bashir Gentile dai na hannun dama ne ga tsohon gwamnan jihar “Ibrahim Shekarau” kuma mai taimaka wa shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a yanzu haka.
Kamar yadda Jaridar ta rawaito cewa, bayan yunkurin kama Gentile ya ci tura wanda a yanzu rundunar ‘yan sandan ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi kan karar da aka shigar a kan sa.
A lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar “SP Abdullahi Kiyawa” ya bayyana cewa, ba shi da masaniya kan gayyata ko shirin kama Bashir Gentilen.
Sai dai kuma “SP Abdullahi Haruna Kiyawa” ya fadi cewa, zai kara yin bincike kan lamarin, a baya-bayan nan da dama daga cikin masu sukar gwamnan suna fuskantar tuhuma a gaban Alkalai bayan ‘yan sanda sun kama su.
Daga cikin mutane masu sukar gwamnatin da aka cafke sun hada da Muaz Magaji da Abdulmajid Danbilki Kwamanda, wanda a halin yanzu ya na gidan yari sakamakon kasa cika sharudan beli da aka gindaya masa.