Advertising
Advertising
Labarai

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya amince da fitar da Naira Miliyan 50 domin bincike kan ciwon Koda

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya
amince da bayar da tallafin Naira miliyan 50 ga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri “UMTH” domin gudanar da bincike kan yaduwar cutar koda a jihar.

Advertising

Babban Daraktan asibitin “CMD na UMTH”
Farfesa Ahmed Ahidjo, ya bayyana yadda Babagana Zulum ya shiga cibiyar koda ta asibitin, yayin wata hira da manema labarai a Maiduguri a jiya Laraba.

A kwanan nan mai girma gwamnan Borno ya
amince da tallafin bincike na naira miliyan 50 ga cibiyar mu ta koda domin mu gudanar da bincike kan cututtukan koda da suka zama ruwan dare a wannan al’umma.

Bincike wani bangare ne na aikinmu a nan kuma muna gudanar da shi, binciken cutar daji shi ma
fifikonmu ne an nakalto Mista Ahidjo a cikin
rahoton.

Advertising

CM D ya kara da cewa, rahoton ya bukaci sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da suyi koyi da irin nagartar gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa, hukumar ta UMTH ta hada da samar da ayyukan jinya da kuma horo da bincike da zasu taimaka wajen dakile cututtuka masu yaduwa.

Mu kwararru ne a fannin ilimi don haka ayyukan asibiti, horarwa da bincike an hada su a kowane fanni na ayyukan asibitin, inji shi.

Mista Ahidjo ya bada tabbacin cewa, asibitin zai cigaba da jajircewa wajen ganin majinyata a shiyyar Arewa maso Gabas sun samu ingantattun ayyuka.

A halin da ake ciki kuma, kwamitin ministoci a karkashin jagorancin babban sakatare na ma’aikatar lafiya “Mamuda Mamman” wanda
ya kammala aikin tantance ayyuka da ayyuka
na musamman a asibitin ya bayyana gamsuwa da abin da ya faru a kasa.

Daga abin da muka gani zan iya shaida cewa, UMTH wata cibiya ce ta kwarewa ina mai tabbatar muku da cewa, idan muka cigaba da kiyaye wannan dabi’a, yawon shakatawa a Najeriya zai zama tarihi,” inji Mista Mamman a cikin rahoton.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button