Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Na taba soyayya da tsohuwar jarumar kannywood Fati Muhammad a shekarun baya, cewar Lawan Ahmad

Na taba soyayya da tsohuwar jarumar kannywood Fati Muhammad a shekarun baya, cewar Lawan Ahmad

Ficaccan jarumin masana’antar kannywood wanda yake sharafin sa a shirin nan mai dogon zango na Izzar so wato Lawan Ahmad, ya bayyana cewa ya taba soyayya da tsohuwar jarumar kannywood Fati Muhammad a shekarun baya.

Advertising

Kamar yadda jarumi Lawan Ahmad yace, a wancan lokacin da suka yi soyayyar da Fati Muhammad har abin nasu ya fara karfi, wanda har manya sun shiga lamarin nasu ana maganar aure.

Sai dai kuma Lawan Ahmad yace, ana tsaka da yin maganar auren ne sai maganar ta wargahe domin Allah bai yarda zasu zama ma’aurata ba, inda yace tun wannan lokacin bai kara soyayya da wata ‘yar fim ba.

Jarumin Lawan Ahmad ya bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da BBC Hausa a wata shira da suka yi a shirin su na daga bakin mai ita.

Advertising

Inda a lokacin BBC ta tambayi Lawan Ahmad cewa, ko ya taba soyayya da wata jaruma a masana’antar kannywood sai ya basu amsa da cewa a, a.

Har ma yake cewa: Mun taba soyayya da Fati Muhammad wacce har maganar aure ma ta dan shiga tsakaninmu da ita, toh amma da yake ka san komai nufi ne na Ubangiji, a wancan lokacin Allah bai yi ba. Shikenan ita ce kadai muka yi soyayya da ita, amma daga ita gaskiya ban kara soyayya da wata ‘yar fim ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button