Labarai
Tirkashi: Wani Limamin Masallacin Juma’a ya ajiye limanci sabo da zai tsaya takara a Katsina
Babban Limamin Masallacin Juma’a na GRA a Jihar Katsina Imam Muhammad Hashim ya ajiye mukamin limancin sabo da zai tsaya takara.
A wasikar ajiye limancin da ya rubuta, mai ďauke da kwanan watan 24 ga Maris, Mallam Hashim ya yi addu’ar Allah Ya rubuta masa ayyukan alherin da ya yi a cikin ayyukansa.
Wani bangare na wasikar, wacce Daily Nigerian Hausa ta gani ya ce, ” i Muhammad Hashim (Liman) na ake mukami na na limancin Babban Masallacin Juma’a na GRA sabo da tsaya wa takara da zan yi.
“Ina fatan Allah SWT Ya rubuta mana ayyukan mu na alheri a cikin ibadun mu da mu ka gabatar, Ya yafe mana kusa-kuren mu Amin.
A cikin wasikar, mai dauke da sa hannunsa, Hashim ya nemi yafiyar yan kwamitin masallacin da ma al’umma baki d’aya.