Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 18 daya kashe kanwar mahaifiyar sa a Kano

'Yan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 18 daya kashe kanwar mahaifiyar sa a Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta cafke wani mai shekara 18 da haihuwa Abdulsamad Suleiman, bisa zargin kashe kanwar mahaifiyarsa Rukayya Jamilu ya kuma raunata yayanta kanana guda biyu a gidanta na aure.

Advertising

Lamarin ya faru ne tun a watan Fabrairu, lokacin da yan sanda suka iske gawar marigayiyar shame shame cikin jini, bayan mijinta ya kai rahoto cewa ya dawo gida ya tarar da mai dakin nasa a wannan hali da misalin karfe 8 na dare.

Nan da nan Kwamishinan ‘yan sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya sa aka garzaya da matar da yayan nata asibitin Murtala, inda likitoci suka tabbatar ta rasu, yayan kuma aka cigaba da kula da lafiyarsu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP
Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Laraba
da daddare, tuni dai ‘yan sanda sun kama wanda ake zargi Suleiman da abokinsa Mu’azzam Lawan, dan shekara 17, dukkan su mazauna unguwar Dorayi Charanci ne.

Advertising

Kiyawa yace, an cafke sune sakamakon binciken sirri da jami’an ‘yan sanda da hadin gwiwa da na ‘yan sandan farin kaya DSS suka yi.

Sannan yace, Suleiman ya amsa laifin sa na bugawa marigayiya Rukayya tabarya a ka lokacin daya kai mata ziyara ya kuma yi yunkurin sace mata wayoyinta na salula har guda uku yayin data ke kwance a kan gadonta.

Ya kuma amsa cewa, ya baiwa abokin nasa
waya guda daya kyauta, wacce ya sayar da ita N2,000, shi kuma Suleiman ya sayar da sauran biyun kan N12,000.

SP Kiyawa dai yace, za’a gurfanar da su a gaban kotu idan an kammala bincike, ya kara da cewa Kwamishinan ‘yan Sanda Dikko yaci alwashin cigaba da zakulo da hukunta duk wasu masu laifi a jihar Kano, inda sai dai ko su dena ko kuma su bar jihar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button