Advertising
Advertising
Labarai

Asirin wani magidanci ya tonu bayan ya dirkawa ‘yar kanin sa cikin shege

Asirin wani magidanci ya tonu bayan ya dirkawa 'yar kanin sa cikin shege

A wani labari da muka samu daga shafin Hausaloaded sun ruwaito cewa, wani magidanci ya dirkawa ‘yar kanin sa cikin shege.

Advertising

Mun sami wallafar labarin kamar haka.

Wani magidanci dake zaune a karamar hukuman Dala dake jahar Kano, ya dirkawa wata marainiya wacce take ‘ya a gurinshi ciki, wacce yarinyar tana da kimanin shekara 15 a duniya, inda ya ribaceta da lemun kwalba.

An ruwaito cewa kafun ya bata lemun sai da ya kwaya aciki sannan ya bata nan take ta kama bacci shi kuwa ya afka mata.

Advertising

Bayan sati Biyu da faruwan lamarin matar sa wacce take rike da yarinyar, ta fara ganin wasu alamu a tattare da yarinyar, inda ta garzaya asibiti da yarinyar don yi mata gwaji, anan ne aka tabbatar mata da ‘yarta tana da juna biyu inda suka takura yarinyar ta fada, sai ta amsa da cewa Baba ne.

Magidancin ya shaidawa matar tashi cewa tayi hakuri lallai shedan ne ya ribance shi kuma hakan ba za ta sake aukuwa ba.
Daga Muhammad Inuwa Zaria.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button