Kotu ta yi watsi da ƙudirin gwamnatin Faransa na rufe wani masallaci.
Kotun kasar Faransa ta rushe kudirin gwamnatin kasar na rufe wani masallaci da ke a birnin Bordeaux.
Lauyan kungiyar masallacin Al Farouk, Sefen Guez Guez, a ranar Laraba ya ce kotun Bordeaux Administrative ta yi watsi da kudirin gwamnatin na ranar 14 ga watan Maris na rufe masallacin har tsawon watanni 6.
Ya lurar da cewa hukuncin kotun wani babban cigaba ne akan yadda gwamnati ta ke rufe masallatai ba bisa ƙa’ida ba. Ya kara da cewa masallacin yana zama a matsayin wurin haɗuwar musulmai.
An rufe masallacin Al Farouk da ke yankin Pessac kusa da garin Bordeaux bisa zargin shi da kare musuluncin tsageranci da kuma yada akidar salafanci.
A watan Augusta, hukuma mafi karfi ta kundin tsarin mulkin Faransa ta amince da wata doka mai cike da ruɗani wacce aka dinga caccaka kan nuna wariya ga musulmai.
Majalisar dokokin ƙasar ta Amince da dokar a watan Yuli duk da yadda wasu daga cikin ‘yan majalisar su ka nuna adawa da dokar.
Gwamnati ta yi iƙirarin cewa maƙasudin dokar shine ƙara ƙarfafa “addinin Faransa” sai dai ma su sukar dokar su na ganin cewa dokar ta tauye haƙƙin gudanar da addini ga musulmai sannan ta ware su.