Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin Nageriya sun kama manya-manyan sassanonin ‘yan ta’adda a dajin Sambisa tare da kwace makaman su

Sojojin Nageriya sun kama manya-manyan sassanonin 'yan ta'adda a dajin Sambisa tare da kwace makaman su

Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai “OPHK” sun samu gagarumar nasarar kame wasu manya manyan sansanonin ‘yan kungiyar ISWAP a Ukuba/Camp Zairo a dajin Sambisa.

Advertising

Daraktan yada labarai na rundunar sojinNijeriya “Bernard Onyeuko” a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Abuja yace, dakarun sun kuma kwace makamai da ga gurin ‘yan ta’addan.

Onyeuko yace, rundunar ta samu wannan nasara ne a jiya Alhamis a wani sintiri da suka yi mai sunan “sintirin share sahara”.

Ya kara da cewa, dakarun ne suka gano ‘yan ta’addan sannan suka kwace sansanonin na su, inda bayan sun tsere sai dakarun suka kwashe
makaman su.

Advertising

Bayan nan yace, bayan bincike mai zurfi da kuma kewaye wajen sai jajirtattun sojojin mu suka dirar musu inda suka tsere, su kuma dakarun suka kwashe makaman su.

Daga makaman sun hada da Tankar yaki, bindiga mai tsayin 155m, bindigar Bofors, Tirela guda daya, bindiga mai tsayin 122mm da bindigogi masu tsayin 105mm.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button