Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin Nageriya sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda a dajin Sambisa

Sojojin Nageriya sun tarwatsa maboyar 'yan ta'adda a dajin Sambisa

Har yanzu dai Sojojin Nageriya suna aikin da ya dace kan ‘yan ta’addan da suka addabi Nageriya musamman Arewacin kasar.

Advertising

Wanda a yanzu muka sami labarin cewa, Akalla yan ta’adda 50 aka kashe a wani hari da dakarun Operation Desert Sanity suka kai a Chingori, Alafa, Darussalam, Akram, Kuraba, da Ukuba wanda duka yankuna ne dake cike da yan ta’addan ISWAP/Boko Haram.

Dakarun kuma sunyi nasarar kwato makamai da dama da kuma motocin yaƙi a wuraren ɓuyan yan ta’addan.

Dakarun 402 Special Forces Brogade, Wadanda suka haɗa da 134 SF Bn, 198 SF Bn da kuma 199 SF Battallions ne suka yi wannan ƙoƙarin kuma sukai nasara.

Advertising

Wannan cigaba ta bayyana irin namijin ƙoƙarin da dakarun ke yi na ganin an kawo karshen ta’addancin ISWAP/Boko Haram. Suna karkata farmakin su a yanzu zuwa maɓoyar yan ta’addan dan kawo karshen ta’addancin su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button