Advertising
Advertising
Labarai

Dan Ministan Sadarwa Isah Ali Pantami da aka sace a jihar Bauchi ya bayyana

Dan Ministan Sadarwa Isah Ali Pantami da aka sace a jihar Bauchi ya bayyana

Dan gidan Ministan sadarwa da tattalin arzikin Sheikh Isah Ali Pantami wanda ake zargin an sace shi a a garin Dambam daya daga cikin kananun hukumomin jihar Bauchi.

Advertising

A ranar Alhamis ne a dandalin sada zumunta aka yi ta yayata cewa anyi garkuwa da dan Ministan a kusa da ginin NIDB da ke Bauchi.

Daya daga cikin malaman dan gidan Isah Ali Pantami ta shaida cewa, mun fito ne daga gidansu ya dawo gida yanzu an same shi a Dambam.

Wadanda suka sace shi suka ajiye shi a shingen binciken jami’an tsaro, daga nan ne aka dawo da shi gida.

Advertising

Da daddare aka sanar damu cewa, an sace shi amma mun godewa Allah Madaukakin Sarki wadanda suka sace shi suka yar da shi.

Babban Limamin Masallacin Jum’a na Minista Pantamin dake Bauchi, Imam Hussaini ya tabbatar da cewa yaron yanzu haka yana gida.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi “Mohammed Ahmed Wakil” ya bayyana cewa, ba’a kai rahoton lamarin ga rundunar su ba.

Ya kara da cewa, mun tuntubi dukkan jami’an ’yan sandan dake Bauchi suka ce ba’a kai rahoton lamarin ba, koda ya faru ba mu sani ba.

Abin da muke bukata daga jama’a shi ne su taimaka mana da sahihan bayanai game da masu aikata laifi a tsakanin alu’mma don daukar matakin da ya dace, kuma idan akwai wata matsala suyi maza su kai rahoto ga ’yan sanda.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button