Advertising
Advertising
Labarai

Dan lelen Shugaba Buhari Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar APC na kasa

Dan lelen Shugaba Buhari Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam'iyyar APC na kasa

Tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa,
Abdullahi Adamu, ya zama sabon zababben
Shugaban Jami’ya mai Mulki a yanzu ta APC na kasa.

Advertising

Abdullahi Adamu wanda shine Sanata mai wakiltar Nassarawa ta Yamma, ya zama Shugaban jami’yar na kasa tun bayan da aka rushe shugabancin Adams Oshiomole, shekara
daya da wata tara da ya gabata.

An zabi Sanata Adamu ne ta hanyar maslaha inda dukka yan takarar kujerar suka janye masa a wajen Babban Taron APC da ya gudana a dandalin Eagle Square a Abuja a jiya Asabar.

Tun tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa kusoshin jam’iyar cewa, shi Sanata Adamu ne dan takarar sa na shugabancin jam’iyar a matakin kasa.

Advertising

Tuni kuma gwamnonin APC da sauran masu
ruwa da tsaki na jam’iyar suka amince da
bukatar ta Buhari.

Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru,
wanda shi ne Shugaban kwamitin zaben shi ya sanar da Sanata Adamu a matsayin shugaban jami’ya na kasa bayan da duk kusoshin jam’iyar da nasu ruwa da tsaki sun amince.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button