Advertising
Advertising
Labarai

Matar data haifi jaki a kwanakin baya ta fara korafi kan mutane sun fara daina sayan abincin ta

Matar data haifi jaki a kwanakin baya ta fara korafi kan mutane sun fara daina sayan abincin ta

Matar data haifi jaririn jaki a ‘yan kwanakin nan ta fara fuskantar kalubale da dama bayan afkuwar mummunan lamarin nata.

Advertising

Matar tana sana’ar sai da abinci domin ta sami kudin da zata rufawa kanta asiri tana da ‘yaya goma sha daya 11, kuma Mijin ta ma ba karfi gare shi ba.

Tun a lokacin da matar ta haifi jakin mutane suka daina dayan abincin ta, labarin haihuwar jakin da tayi ya karade ko ina har wasu ma suke tausaya mata tare da taimakon ta, amma sai aka sami wasu kuma suna kyamatar ta.

Amma wata majiya wacce ta bukaci a sakaya sunan ta ta shaida cewa, a yanzu haka dai matar bata samin ciniki akan sana’arta kamar da.

Advertising

A cewar majiyar: Wasu mutane sun fara kyamarta. Wasu suna ganin matsalar zata taba abincin da take siyarwa ko kuma wanda ya yi mata asirin ya yi akan kayan abincinta.

Wannan dalilin ne yasa suka dakata da siyan abincin.

Akwai wacce muka tattauna da ita kuma a baya kusan kullum sai ta siya abincinta, amma sai ta kada baki tace.

Tabdijam! Jaki fa ta haifa! Ni dai gaskiya tun daga ranar da ta haifi jaki na ji ba zan samu natsuwa ba, ko da na siya abinci a wurinta.

Saboda ina tsoron abinda zai faru da ni. Kada ya zo abinda take magana akan cewa an tura mata ya fada kan abincin da take siyarwa.

Ta ci gaba da bayyana cewa ko wani ta ji zai siya sai ta bashi shawarar kada ya siya don gudun abinda zai kai ya dawo.

To, Allah dai yasa mu dace, ya kuma kiyaye gaba. Ameen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button