Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’adda sun hallaka wani ma’aikaci tare da hana jirgin sama rashi a jihar Kaduna

A jiya Asabat ne wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka dira a filin tashi da saukar jiragen sama inda suka hana jirgi tashi.

Advertising

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa, jirgin wanda aka tsara zai tashi zuwa Jihar Legas da misalin karfe 12:30 na rana, bai iya tashin ba sabida ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai, sun mamaye filin titin jirgin.

Jaridar ta jiyo cewa, ma’aikata da fasinjoji sun
ranta ana kare domin tsira da ransu lokacin da ‘yan ta’addan suka shiga filin titin jirgin.

Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun kashe wani ma’aikacin Hukumar kula da Sararin saman Nijeriya, NAMA.

Advertising

Sai dai kuma a cewar Nigerian Tribune, an
kawo sojoji filin jirgin saman domin samar da
tsaro.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button