Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: Yadda wata mata ta mutu kuma ta dawo a kasar Ghana.

Wata budurwa mai suna Zuweira da rahotanni suka bayyana mutuwarta, daga bisani kuma ta farfado ‘yan mintuna kadan kafin a binne ta, ta sake mutuwa. likitocin asibitin Ridge dake Accra kasar Ghana sune suka tabbatar da mutuwar budurwar a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris.

Advertising

A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana,an ga Antin zuwaira, Rabu wacce ita ce ta bada bayanin cewa Likitoci sun tabbar da mutuwar Zuweira a inda aka shirya yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulmi ya tanada, Rahotanni daga Ghanaweb. Ta ce an shirya duk wani shiri da ya dace kawai likitoci su ka kira cewa Zuweira ta farfado

Rabi Dan-Alpha Sharubutu ta tabbatar da cewa diyarsu ta sake rasuwa, tana mai cewa:

“Na gode wa kowa da kowa bisa addu’ar da kuka yi wa ‘Yar uwata. Amma ta koma ga mahaliccin ta yau, Allah ne mafi sani. Allah ya sa ta huta, ta ce.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu a game da wannan al’amari.

Advertising

Gimbiya Umma ta ce: ”Allah ya jikanta Yasa Aljanna ce makoma.”

Adam Ibrahim ya ce:Allah ya jikan ta da Rahama.”

AlhajiGaza Gudliving ya ce: ”Allah Ya jikanta da Rahama”

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button