Anyi baran-baran bayan Amarya ta gano Angon da zata aura bashi da gashi akan kan sa sai sanko
Anyi baran-baran bayan Amarya ta gano Angon da zata aura bashi da gashi akan kan sa sai sanko
An tarwatse a wani biki da ake gudanarwa a india bayan Amaryar taki yarda a daura auren ta da Angon nata sabida ta gano yana da sanko a kan sa.
Shirye shiryen aure abu ne da ya zama ruwan dare a Indiya amma duk da iyalan ma’auratan sun jima suna tsarawa da tattaunawa akan bikin, amma duk da haka sai da aka samu matsala.
Kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwauto, wani lokaci daga bangaren amarya wani lokacin kuma akan sami tangarda sakamakon rashin sanin wanda za’a aura.
Wani daurin aure da aka yi kwanan nan a Gundumar Etawah dake birnin Kanpur a jihar Uttar Pradesh, inda Amaryar taki amincewa da’a daura aure bayan ta gano cewa angonta yana da sanko.
A cewar jaridar Times of India, komai yana tafiya yadda aka tsara ne inda an riga an yi musayar furanni tsakanin ma’auratan, amma sai aka sami tangarda a lokacin da Amaryar ta lura cewa Angon nata da zata aura ya sanya kayan gargajiya da yawa a kansa don boye sankon sa.
Nan take ta fada wa wani a cikin ’yan tawagarta don bincika ko a zahiri yana da sanko ko kuma yana sanye da sumar bogi ne.
An bayyana cewa, matar ta kadu da wannan fallasa sai ta tunkari Angon a kan lamarin, inda bayan ta tabbatar da cewa ba shi da suma sai sanko sai ta sume nan take a wajan.
A lokacin da Amaryar ta dawo hayyacinta sai taki zama a cigaba da yin bikin auren inda ta sanar da danginta cewa, ba zata auri mai sanko ba a kowane hali.
Yan uwan Amaryar sun yi kokarin gano wani dalilin matar ba ya ga na sanko amma babu inda suka rarrashe ta, don haka basu da wani zabi illa su gaya wa dangin ango cewa an fasa yin daurin auren.
Hakan bai yi wa ’yan uwan Amgon dadi ba kuma an jama’a sun yi ta cece-kuce, wanda a karshe dangin amarya suka zargi dangin ango da yaudarar su ta hanyar rashin bayyana halin da gashin nasa ke ciki.
Inda a karshe dattawan kauyen sun shiga tsakanin ma’auratan ta hanyar kwantar da hankulansu, daga bisani iyalan ma’auratan biyu suka watse.
A cewar rahoton ’yan sandan yankin bangarorin biyu sun kammala gabatar da korafin junansu, inda bangaren dangin Amaryar suke ikirarin an yaudare su.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan yankin ya bayyana cewa, daga baya ma’auratan biyu sun janye kokensu tare da warware matsalar a tsakaninsu.