Advertising
Advertising
Labarai

Duk da harin da aka kai jirgin kasa sai da Buhari yaje kallon wasan Kwallon kafa tsakanin Nageriya da Ghana

Duk da harin da aka kai jirgin kasa sai da Buhari yaje kallon wasan Kwallon kafa tsakanin Nageriya da Ghana

Kamar yadda shafin Daily Nigeriyan Hausa suka wallafa cewa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi kallon kwallon kafa da Najeriya zata fafata da Ghana a Abuja, a wasan neman
gurbin shiga gasar cin kofin duniya a Qatar, inji BBC Hausa.

Advertising

Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta gano cewa, Buhari ya je kallon kwallon kafar ne yayin da kasar ke alhinin harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a jiya Litinin.

BBC Hausa ta rawaito cewa, titin da ya fito daga fadar shugaban kasar har zuwa filin kwallon kafa dake birnin Abuja ya kasance shiru babu ababen hawa sabida wucewar shugaban.

Gwamnati ta samar da tikitin shiga kallon wasan kyauta ga ‘yan Najeriya domin nuna goyon baya ga ‘yan wasan Najeriya.

Advertising

Duk kasar da aka ci tsakanin Najeriya da Ghana ba zata tafi gasar cin kofin duniya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button