Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Falalu a Dorayi ya tofa albarkacin bakin sa kan ‘yan ta’addan da suka tada Bam a jirgin kasa tare da yin fashi a ciki

Falalu a Dorayi ya tofa albarkacin bakin sa kan 'yan ta'addan da suka tada Bam a jirgin kasa tare da yin fashi a ciki

Kamar yadda a dazu muka kawo muku labarin cewa, a daren jiya Litinin ne dai wasu ‘yan ta’adda suka tashi bam a kan layin dogo na jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, inda suka samu nasarar tsayar da jirgin.

Advertising

To a yanzu kuma mun sami wata wallafa daga shafin shahararran Daraktan masana’antar kannywood Falalu A Dorayi akan abin da ‘yan ta’addan suka aikata.

Falalu a Dorayi ya wallafa bayanin kamar haka.

An kashe wasu an debi wasu wasu sun bata.

Advertising

Ya Ubangiji KAjikan wadanda suka rasu, wadanda aka dauka Allah KA tsare mutuncinsu ka basu sauki da maflta.

KA bawa iyalai da ‘Yan uwa hakuri.

Jiya har Karfe 3:00 Muna waya da wanda abin ya ritsa da su kafln a kawo su kaduna.

Anyi rashin imani,

Allah ya tsare gaba, ya karemu da iyalanmu da
al’umma baki daya. Allah ya tona asirin wadannan ‘Yanta’adda.

Su Kuma Shugabanni Allah ya tayar dasu daga baccin da suke su dubi al’umma. Amin.

Babu bin titi, babu train.

Wannan ita ce wallafar da Falalu A Dorayi ya yi cikin wani rubutu a shafin sa na sada zumunta instagram akan ‘yan ta’addan da suka saka Bam a hanyar jirgin kasa tare da yin fashi a ciki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button