Yahaya Bello Gwamnan jihar Kogi shine zai iya kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi, cewar Hamisu Breaker
Yahaya Bello Gwamnan jihar Kogi shine zai iya kawo karshen rashin tsaron da ake fama da shi, cewar Hamisu Breaker
A wani bayani da mawakin masana’antar kannywood Hamisu Breaker ya wallafa a shafin sa na sada zumunta instagram, wanda Ibrahim Adamu Director Media and Publicity YBN yasa hannu a kasa.
Mawaki Hamisu Breaker ya wallafa bayanin kamar haka.
A Bawa Yahaya Bello daman shugabantar harkokin tsaro a wajen babban taron APC na kasa, ya nunawa duniya cewa kwararre ne shi a iya bada tsaro ga al’umma.
Hakikanin Gaskiya Sai bayyana su ke a tare da maigirma gwamna Yahaya Bello. A can baya mun Dade muna fadawa al’umma cewa Yahaya Bello ya kai matsayin field Marshall a gidan soja in dai a bangaren iya bada tsaro ne.
Sannan yace, Sau da dama muna anfani da wannan kafa ta Facebook da sauran kafafen sada zumunta na zamani domin mu nunawa duniya cewa Yahaya Bello babu na biyun shi wajen iya shugabanci da tsaro a duk kasar nan, manuniya ce ta nuna yau idan kana shakkar abubuwan da muke fada ga me da Yahaya Bello wannan kawai ta Isa hujja.
Tsaro ita ce ko wacce al’umma take bukata fiye da komai a wajen kowani shugaba, hakika duk shugaban da yafi mayar da hankali kan matsalolin tsaro ya tabbata wannan shugaba ya San mene ne shugabanci, yau idan kaje jihar kogi zaka tabbatar da cewa babu wanda ya dace da ya zama shugaban kasa a Najeriya kamar Yahaya Bello.
Idan muka lura da Najeriya a yanzu ba tada matsalar da ya wuce matsalolin rashin tsaro ko A can baya Kafin na fahimci wane ne Yahaya Bello ban san da cewa nagatarsa ta kai har ya iya kawo zaman lafiya a jihar kogi ba. Amma biyo bayan bincike da nazari mai zurfi da na yi, sai na gano lallai Yahaya Bello Shugaba ne jajirtacce irin wanda kowacce al’umma ta ke buƙata.
Yahaya Bello yana da salon shugabancinsa sannan kuma ya na tafiya ne a bisa tsarin Adalci da Gaskiya da kuma son cigaba ga matasa, ganin yadda aka kammala taron APC a Abuja lafiya ya kara nuna mana cewa mun gamsu da Yahaya Bello da irin salon mulkin sa idan ya rike Najeriya zai kawo tsaro mai inganci a kasa da taimakon Allah.
Shin kuna ganin Gwamna Yahaya Bello na da rawan dazai taka a halin tsaron da ake ciki.