Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’adda sun tashi Bam a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da fasinjoji 970 a ciki

'Yan ta'adda sun tashi Bam a cikin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da fasinjoji 970 a ciki

A daren ranar Litinin din nan ne dai wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka tashi bam a kan layin dogo na jirgin kasan Abuja Kaduna, inda suka samu nasarar tsayar da jirgin cak.

Advertising

Wasu sahihan majiyoyi ne suka tabbatar da harin ga jaridar DAILY NIGERIAN a daren na Litinin, inda suka ce harin ya faru ne a wani waje tsakanin Katari da Rijana.

Daya daga cikin fasinjojin ya tabbatar da harin ta wayar salula yace, maharan sun kewaye jirgin suna ta harbin shi.

Duk fasinjojin na kwance a kasa a cikin jirgin a halin da ake ciki yanzu ‘yan ta’addan ne ke
ta harbin kan me uwa da wabi.

Advertising

Muna cikin bala’i inji wani fasinja da yake cikin firgici wasu majiyoyi daga ma’aikatar jirgin kasa
sun tabbatar da cewa, Dawaki fasinjoji 970 a cikin jirgin.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button