Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruma Rahama Sadau tayi Allah ya isa ga Shugabannin Kasar Nageriya kan matsalar rashin tsaro a Arewa

Jaruma Rahama Sadau tayi Allah ya isa ga Shugabannin Kasar Nageriya kan matsalar rashin tsaro a Arewa

Ficacciyar jarumar masana’antar kannywood da Nollywood Rahama Sadau tayi Allah wadai kan harin da ‘yan ta’adda suka kai jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, kamar yadda Hausaloaded suka ruwauto.

Advertising

Idan zaku iya tunawa a daren ranar Litinin ne wasu ‘yan bindiga suka dasa Bam a wani jirgin kasa mai dauke da fasinjoji sama da 970 wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna, inda suka kashe mutun 8 da yin garkuwa da mutun 30 tare da raunata mutane da dama daga cikin jirgin bayan sun yi nasarar tsaida shi.

Jaruma Rahama Sadau ta tofa albarkacin bakin ta kan lamarin inda take cewa, Najeriya kasa ce wacce ta gaza kuma shuwagabannin ta suka gaza kare rayukan al’umma.

Sannan kuma Rahama Sadau ta kira shugabannin Najeriya da wadanda suka gaza tabuka komai ga yan kasar.

Advertising

Jaruma Rahama Sadau ta dora wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta Twitter a cikin harshen turanci, inda ta magantu akan cewa Najeriya na fama da kalubalen rashin tsaro.

Inda a karshe jaruma Rahama Sadau tayi Allah ya isa har sau uku 3 ga mahukuntan Kasar Nageriya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button