Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, cewar Rahama Sadau

Yadda na tsallake rijiya da baya a harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, cewar Rahama Sadau

Shahararriyar jarumar masana’antar finafinai
ta Kannywood Rahama Sadau da ‘yan
uwanta sun godewa Allah da ya raya ta ta
tsallake rijiya da baya, daga harin jirgin kasan
Abuja zuwa Kaduna.

Advertising

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a ranar
Litinin ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan jirgin
kasa da ya taho zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka jefa bama-bamai da yin harbe-harbe lamarin da ya sanya wasu fasinjojin suka rasu, wasu suka samu raunuka inda da yawa kuma sun bata ba’a gan su ba.

Sai dai kuma Rahama Sadau ta wallafa a shafin ta na twitter cewa, an shirya zata shiga jirgin tare da ‘yar uwarta amma suka yi latti basu samu guri ba, amma kuma bayyana cewa ta na da abokai da suka shiga cikin jirgin kuma wadanda harin ya rutsa da su.

Ta rubuta, Ni da ‘yar uwana mun so kasance
a cikin jirgin da aka kai hari a daren jiya amma muka rasa shi.

Advertising

Jarumar ta yi amfani da damar wajen baiwa
magoya bayanta shawarar su karbi katin zabe na dindindin (PVC) da kuma tabbatar da kirga kuri’unsu.

Mu (AREWA) mu muka kawo kanmu wannan halin mun zabi Shugabannin yanzu don su magance Mana Matsalar tsaron data addebe mu, amma hakan taki samuwa to don haka idan muka mallaki katin zabe sai mu zabi Shugabanni na gari.

A yau an jibge jami’an tsaro masu tarin yawa a film wasa na MKO Abiola na fahimci cewa, Nijeriya tana iya yin maganin wannan matsalar kawai sun zabi suyi watsi da mu aita kashemu, su babu ruwan su.

How i cross a well and back in a railway
attack-Rahma Sadau.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button