Advertising
Advertising
Labarai

Zan sayar da Motata domin na biyawa Saurayin kudin Digiri na 2 kuma na bashi kudin kasuwanci, cewar wata Budurwa

Wata Budurwa wacce tayi abin mamaki ta dauki hankulan jama’a da dama a yanar gizo-gizo inda take cewa, zata sayar da Motar ta domin ta biyawa saurayin ta kudin digiri na biyu wato “Masters” kamar yadda muka sami labarin daga shafin Hausaloaded.

Advertising

Sannan kuma Budurwar ta kara da cewa, sauran kudin da ya rage a wajan ta zata kafawa saurayin nata kasuwanci, inda har take cewa ya cancanci komai.

Ga dai yadda cikekken rahoton yake.

Ina son na siyar da motata domin biyawa saurayi na kuɗin zangon ƙarshe domin ya samu ya kammala digirin sa na biyu.

Advertising

A cewar Joy Turamuhawe: A yayin wata zantawa da TUKO.co.ke, Turamuhawe ta bayyana cewa, ita ta aminta da cudeni in cudeka.

Na ga mazaje da yawa waɗanda su ka yiwa ‘yan matan su abubuwa da dama saboda suna ƙaunar su, sannan ni na yarda da cuɗeni in cuɗeka. inji Turamuhawe.

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan wannan bayanin na Budurwar, ga kadan daga cikin su.

Joansheenah yace: Cikin hawaye abin zai kare.

Brökë_C3lëbrïty yace: Idan har da gaske ne to ina so na zama saurayin ki. Ina mamaki yadda wani ya ke ƙoƙarin neman digiri na biyu amma bai da aikin yi.

Marvin k yace: Gaskiya ka da ki siyar da motar ki. Idan zai yiwu ki amshi bashi, sannan ki yi amfani da motar ki a matsayin jingina, kowane banki zai baki bashin kuɗi daganan sai ki dinga biya a hankali a hankali, saboda za ki buƙaci motarki sannan saurayin ki yayi sa’ar samun ki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button