Advertising
Advertising
Labarai

An kama wata tsohuwa tare da matashin da tasa ya kwakule idanun Almajiri domin tayi masa Layar zana

An kama wata tsohuwa tare da matashin da tasa ya kwakule idanun Almajiri domin tayi masa Layar zana

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta cafke wani matashi dan shekara 17 mai suna Isah Hassan
mazaunin Dantsinke layin Rimin Hamza a Karamar Hukumar Tarauni, bisa zargin cire idanun wani almajiri dan shekara 12 mai suna Mustapha Yunusa.

Advertising

Kakakin rundunar “SP Abdullahi Haruna Kiyawa” a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba da daddare yace, an kama yaron ne a ranar Talata da taimakon yan sintiri na unguwar.

Yace, a ranar 20 ga watan Maris ne suka samu korafin cewa, wani da ba’a san ko waye ba ya kwakule wa almajirin idon sa na dama.

Daga nan ne a cewar Kiyawa sai Kwamishinan ‘yan sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya baiwa rundunar Puff Adder umarnin a nemo wanda ya yi aika-aikar.

Advertising

Ya kara da cewa, bayan an dau lokaci ana bincike sai rundunar ta samu damar cafke Hassan, wanda ya amsa laifin sa cewa wata
tsohuwa ce tace ya samo idon mutum ta hada masa layar zana.

A cewar wanda ake zargin yace, ya samu abokin sa dan shekara 16 ne Sani Abdulrahman cewa yana so ayi masa layar zana, shine shi kuma ya kai shi wajen kakarsa Furera Abubakar domin ta hada masa layar.

Hassan yace, da ya same ta sai Furera tace ya samo idon mutum a matsayin sinadarin da zata hada masa layar zanan, shine shi kuma yaja wannan yaro zuwa wani jeji inda ya daure masa hannaye ya kuma saka wuka mai kaifi ya kwakule masa idanu na dama.

Ya kara da cewa, bayan ya kawo mata idanun shi ne Furera tace sai ya taba Naira 500 ladan aikin da zata yi masa sai Hassan din ya ce bashi da Naira 500 amma zai kawo mata idan ya samu, inda ita kuma tsohuwar tace yaje ya ajiye idanun.

A karshe dai duk an kame su, inda Kiyawa ya
ce za’a kai su kotu idan an kammala bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button