Advertising
Advertising
Labarai

An yankewa wani makiyayi tsawon shekaru 7 a gidan yari bayan an kama shi da satar shanu 259

An yanke wa makiyayi shekaru 7 a gidan yari
sakamakon satar shanu 259, a yau Alhamis ne wata Kotun Majistare dake Abeokuta ta yanke wa wani makiyayi mai suna Abdullahi Adamu mai shekaru 38 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, bisa samunsa da laifin zamba da satar shanun da suka kai sama da Naira miliyan
43.

Advertising

Adamu, wanda ba’a bayar da adireshinsa ba, an same shi da laifuka uku da suka hada da hadin-baki, zamba da kuma sata.

Da take yanke hukuncin, mai shari’a Olajumoke Somefun, ta ce dukkanin shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar sun tabbatar da cewa, babu tantams wanda a ke tuhuma ya aikata laifin.

Somefun ta bayyana cewa, bayan an samu wanda ake kara da laifi kamar yadda ake tuhumarsa, amma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zabin biyan tarar N250,000.

Advertising

Ta kara da cewa, tarar zata yi aiki ne idan wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo da shanu 259 din da ya sace.

Tun da fari dai dan sanda mai shigar da kara,
ASP Olakunle Shonibare, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Alamutu ta hanyar Rounder a Abeokuta.

Shonibare yace, wanda aka yankewa hukuncin ya hada baki da wani mutum guda, wanda a halin yanzu ya gudu suka sace shanu 259 na mutane bakwai.

Yace, wanda aka yankewa hukuncin makiyayi ne kuma ana bashi shanun mutane ya kiwata, mai gabatar da kara yace Adamu da niyyar damfara sai ya karbi shanun da niyyar kiwata wa amma sai ya mayar da su nashi na kansa da nufin ya hana masu shi.

Haka kuma wanda aka yanke wa hukuncin
ya kwashe shanu 15 da kudinsu ya kai Naira
miliyan 1.5, da kadarar Funmilayo Ogunlana
da shanu 12 da darajarsu ta kai Naira miliyan 1.2, mallakin Jimoh Salaudeen.

Ya kuma saci shanu biyar, wanda kudinsu ya kai N500,000, na Adekunle Adedolapo, da shanu shida, na Kabiru Bankola, N600,000, da shanu biyu, wanda darajarsa ta kai N200,000, mallakar Abeebi Adeyemi.

Mista Shonibare ya lura cewa jimillar duk shanun da wanda aka yankewa laifin ya sace ya kai Naira miliyan 43.9.

A cewar mai gabatar da kara, laifukan da aka
aikata sun Ci karo da sashe na 516, 383 da
390 (3) (6) (a) na kundin dokokin jihar Ogun,
2006.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button