Kashe kashen da ake a Arewa maso Yamma yafi na Arwwa maso Gabas, cewae Gwamna Nasir El-Rufa’i
Kashe kashen da ake a Arewa maso Yamma yafi na Arwwa maso Gabas, cewae Gwamna Nasir El-Rufa'i
Gwamna Nasir El-Rufa’i na jihar Kaduna a yau Alhamis yace, girman kalubalen tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yamma ya fi wanda aka gani a Arewa maso Gabas.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Giwa na jihar Kaduna, inda ‘yan ta’adda suka
addabi mutanen yankin kwanaki biyar da suka gabata, inda aka kashe ko kuma sace mutane da dama.
A cewarsa, noma ya zama ba zai yiwu ba yayin da ake asarar rayuka sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.
Muna ta matsa lamba tun shekaru biyu da suka gabata cewa, sojoji daga sama su rika jefo bamabamai, inda su kuma sojojin kasa su rika harbe duk wani wanda ya tsere wa bam din a dazuka.
Ban yarda cewa akwai wani marar laifi a cikin dajikan ba, Na yi niyyar naga shugaban kasa domin na sake nanata hakan kuma in nemi a kafa shelkwatar rundunar soji sabida yankin
Arewa maso Yamma, in ji shi.
Lokaci ya yi da sojojin saman Najeriya da sojojin Najeriya zasu ba wa ‘yan ta’adda bama bamai ba tare da wanzuwa ba.
Tare da sanarwar da babbar kotun tarayya ta bayar na cewa, wadannan ‘yan ta’adda ‘yan
ta’adda ne, akwai bukatar hukumomin tsaro
su dauki tsauraran matakai domin ganin an kawo karshen wadannan barayin, in ji Mista
El-Rufa’i.
Ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Giwa sakamakon harin ‘yan ta’adda da ya addabe su tsawon kwanaki biyar.
Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.