Labaran Kannywood

Wani saban Faifan Bidiyon tikar rawa da wani uba daga cikin Kannywood keyi ya bar baya da kura.

Wani faifan bidiyon daya daga cikin jarumai iyaye a masana’antar Kannywood kenan Tahir Fagge yana tikar rawa lamarinda ya matukar janyo cece kuce.

Cikin faifan bidiyon dai zakuga yadda jarumin yake chashewa duk da cewar shigar datake jikinsa shigace ta mutunci da kamala domin kuwa har hulace akan jarumin.

Sai dai yadda yake tikar rawa anamai ihu awajan hakan yasa masoyansa da masoya kallon fina finan hausa sunji babu dadi a ransu, domin Tahir Fagge a matsayin uba yake a masana’antar baikamata ace ana ganin irin haka daga gareshi ba.

https://youtu.be/JWbnKreCYbY

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button