Advertising
Advertising
Labarai

‘Yan ta’addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fara tuntubar iyalan fasinjojin da sukayi garkywa dasu kudin fansa

'Yan ta'addan da suka kai hari jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun fara tuntubar iyalan fasinjojin da sukayi garkywa dasu kudin fansa

Kamar yadda kuka sani ‘yan ta’adda sun saka Bam a hanyar jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wanda yake dauke da kimanin Mutane 970 a ciki.

Advertising

Wasu da dama daga cikin Mutanen sun rasa rayukan su wasu kuma sun jikkata, to a yanzu kuma mun sami wani labari daga “Daily Nigerian Hausa” inda suka wallafa wani labari kamar haka.

Yan ta’adda da su ka kai hari kan jirgin kasa a kan hanyar sa ta zuwa Kaduna da ga Abuja a
ranar Litinin, sun fara tuntu bar iyalan fasinjojin da suka yi garkuwa da su.

Iyalin wani da ga cikin fasinjojin da yake hannun ‘yan ta’addan mai suna Abdullahi, sun ce ‘yan fashin dajin sun tuntube su ta wayar salula kuma sun ce musu su shirya biyan kudin fansa.

Advertising

Punch ta rawaito cewa, wani Jibreel Khalil dan uwan Abdullahi din yace duk da basu fadi nawa za’a basu ba, amma dai ‘yan ta’addan sun kira sun kuma ce yana hannun su sannan a shirya biyan kudaden fansa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button